Hacking Facebook Ta Phishing da Yanda Zaka Kare Facebook naka[www.wixardtech.com.ng]
YANDA AKE HACKING NA FACEBOOK TA HANYAR AMFANI DA PHISHING
Dafarko dai ita PHISHING:
wani tarko ne ko Kuma in ce wata
technique ne Wanda ana Amfani DA
shi wurin hacking na Lambar tsaro
(password) na Facebook.
Phishing yanada saukin fahimta da saurin ganewa ga mai karamar kwakwalwa wurin samun phishing page, shiyasa yazama ruwan dare gama gari.
Mafi yawancin mutane ana azabtar da sune ta hanyar amfani da "phishing page" wurin yi musu kutse saboda shi ne yafi bayyana Kuma akafi yarda da shi.
YAYA PHISHING YAKE AIKI?
Phishing dai wata hanyace da masu kutse suke kutse (cracking) Kuma su kofe (copy) sirrikan masu shafin yanar gizo (website), shafin Facebook (Facebook page) da Kuma sacewa masu amfani da Facebook (user's) lambobin sirri (password) da Kuma muhimman bayanai (sensitive information) kamar su credit card, BVN da sauransu.
A cikin wannan rubutun zamu fahimci cewa masu kutse (hackers) suna kirkirar (creating) shafi (page) ne Wanda yayi kamada Facebook logging page tareda wani fake URL na daban kamar "Fakebook.com"
Ko Kuma
"Faecbook.com"
Ko ma duk wani URL Wanda zasu rikitaka su Raina ma wayo da shi yanda zaka Rickice baza kayi tunanin tarko ne aka kafa makaba.
Duk wani mai Facebook (user) da yafada wannan tarko na ire-iren wayannan Shafin (page) bazai taba tunanin ba Ainihin Facebook logging page bane.
Idan kafada a wannan tarkon za a tambayeka da ka sake saka username naka da Kuma password, to Don haka duk mutanen da basu fahimci cewa "PHISHING PAGE" bane sai su saka username dinsu da password nasu, shiyasa cikin sauki masu kutse (hackers) Wanda ya kirkiri (creating) na shafin bogi (phishing page) zai samu username naka da password naka, da duk wani information naka da kasa, shikuma nantake sai ya tafi zuwa Ainihin "Facebook page" yayi maka barazana ko duk abinda yaga dama yayi posting.
BAYANI A DUNKULE
Misali: Yanzu ace Abdu programmer ne Kuma ya kirkiri (creating) wani "Facebook logging page" tareda wani scripts da zai bashi damar samun username da password information na mutane, Abdu Kuma sai yasaka Wannan fake logging page din
👇👇👇👇👇
https://www.facebouk.com/make-money-online-tricks.
Sai Kuma ya kasance Umar Abokin Abdu programmer ne, kawai sai Abdu ya turawa da Umar sako "Assalamualaikum Umar nasu wata sabuwar garabasa Wanda ake samu kudi online cikin sauki" Kai tsaye Umar idan ya duba yaga link "https://www.facebouk.com/make-money-online-tricks-free".
Kawai sai ya shiga to dazarar ya shiga zaiga Facebook logging page, kamar kullum Umar zaisa username nashi da password nashi na Facebook.
Nantake username da password nashi zasu tafi Wurin Abdu, shikenan Abdu yayi hacking na Account din ma'ana zaije ya canja ma Umar password da suna inyazo shiga Facebook nashi taki shiga ko anuna mishi incorrect password,
Inma yayi Forgot password ma za a turawa Abdu ne Don
Tuni yariga ya canja wa Umar number.
YANDA ZAKA KIRKIRI PHISHING PAGE
Yanzu zamu dauki Facebook a matsayin misali
Sharadi! Dole sai kanada kwamfuta (computer)
STEP 2: kadanna Ctrl + U Don kabude source code
STEP 3: kayi copy na source code din sai kayi pasting a cikin "notepad" sa'annan kayi save
STEP 4: kabude notepad dinda kayi save sai kayi Searching na kalmar "action" batareda wannan alamar quotes da nasakaba (" ") idan ka Danna Ctrl + U acikin notepad .
Acikin Facebook logging page, kalmar action ta attribute an sanyata a cikin Facebook logging a matsayin URL to sai ka canja ta zuwa matsayin PHP
STEP 5: Yakamata kasan sunanda zaka sakawa wurin amfani da inspect element idan ka Danna (Ctrl + shift + I acikin chrome)
A wajen mu Email and password ne
STEP 6: Sai kayi Saving din wannan file din as index.html
STEP 7: Yanzu zaka iya samun username da password acikin text suna file din shine phishing.text
Sai kayi creating wani file process.php tareda amfani da wannan code din
👇👇👇
Process.php
YANDA ZAKA SAKA PHISHING PAGE A URL
Idan zaka saka phishing page a URL
yanada kyau ka mallaki abubuwa guda biyu:
1• DOMAIN
2• WEB HOSTING
1) Domin samun free domain ka shiga wannan site din
Zaka iya samun free domain ne a bluehost indai kataba biyan hosting plan nasu
Idan kayi creating domain yanada kyau ka samu hosting da set up name servers nashi.
Amma idan ka dauki bluehost babu wani bukatar sai kayi set up name servers tunda an riga da an setashi
2) Don samun web hosting
Dukkanin wani free hosting panel ana blocking nashi idan kasa phishing page.
Don haka Yaka mata kasami hosting Wanda ake biyan kudi Koda guda ne, duk ba zai wuci ka biya $4 a duk wata.
Nakawo bluehost ne sabida yafi zama amintacce da Kuma aiki mafi nagarta.
Ina baku shawara da kuje ku Sami bluehost shared hosting da domain yanzu.
Idan ka seta domain da hosting, kana iya upload na file din ta hanyar amfani da FTP software.
Shikenan kana iya godawa yanzu.
YANDA ZAKA KARE FACEBOOK NAKA DAGA MASU KUTSE
Dafarko dai ku rage shiga duk wani link da kuka gani, ba kowani link ka gani zaka shigaba kuma ka lura da link din sosai.
ku daina sanya lambobin ku a matsayin password ko kuma 1234 domin masu kutse suna iya chankan password naka ko su sa sunanka ko na babanka ko na budurwar ka ko kuma lambar wayarka don haka a kiyaye.
kuma ba kowa bane zakana gaya musu password naka ba,
kuma ku daina yawan logging Facebook naku aduk wani wayar da kuka karba misali mutum ya karbi wayar abokinshi sai ya shiga Facebook, inyasamu wayar wani ma sai ya shiga sai kasamu mutum yahau Facebook a wayoyi daban daban hakan kuma gaskiya bai dace ba. Yan uwa don Allah kiyaye.
A gaskiya karatun yanada matukar nauyi sai kuyi hakuri da karancin bayanina.
Inda mukayi dai dai Allah yasa ayi amfani da shi inda kuma mukayi kuskure a gafarcemu sabida karancin ilimi.
Wanda bai fahimta ba zai iya yin comment a kasa Don mu mishi Karin BAYANI
Related Posts
Subscribe Our Newsletter




0 Comments to "Hacking Facebook Ta Phishing da Yanda Zaka Kare Facebook naka[www.wixardtech.com.ng]"
Post a Comment