Abubuwa 7 yakamata mutum ya bari in Yanason battery na shi ta jima [wixardtech.com.ng]
ABUBUWA BAKWAI DA YAKAMATA MUTUM YA BARI IN HAR YANASON BATIRI NASHI TA JIMA.
Assalamualaikum yan uwa maza da mata barkan mu da sake saduwa a wannan shafin Mai Albarka Wixard Tech.
A yau munaso muyi muku bayani filla-filla yanda zaku magance matsalar shan chargi da Kuma me yake kawo sanadin wayar mutum ta dinga sha
To dai ga Wasu matakai guda bakwai da In Allah ya yarda in kabisu to kaikam ka kubuta daga wahalan shan chaji.
Ita waya da kuke gani yanzu ta zama wani bari ko ince wani bangare na rayuwarmu Wanda a kullum muna tare da ita,
Wasu wayansu tana hanasu bacci , Wasu tana hanasu cin abinci, Wasu suna neman kudi ta waya, Wasu Kuma suna cutar mutane ta wayar salula, da dai sauransu.
Wayar salula tanada muhimmanci gurin Kiran yan uwa da abokan arziki da Kuma itace hanya Mafi sauki wajen isar da sako ga kowa walau Mai kudi ko talaka.
Amma inda kurar take shine kowa na bukatar wayar da take juriya wajen rike chaji da kyau.
Domin battery itace waya, bazai yiwu ace kanada bukatar wayarka zakayi amfani da shi Kuma kaga ba chaji gaskiya bazaka ji dadi ba.
Battery waya tanada muhimmanci sosai
Don haka gan-ganci da rashin kulawar mu da wayan ne ke nakasa BATIRI na wayan domin akwai ka'idodi da ya kamata mubi wajen kulawa da wayan mu bama bi, inda munabi bazamuyi korafin rashin karfin battery ba.
Yanzu anan ga Wasu matakai guda bakwai da yakamata kubi in har kunaso wayanku ta jima kuna moreshi batareda korafin shan chaji ba
👇👇👇👇👇
1• Kunna Alamar jirgi (AIRPLANE MODE) in kana gurinda network baida karfi.
Dazarar tafiya ko aiki ya kaika inda network ba karfi kawai Dan uwa ka Kunna Alamar jirgi (Airplane mode) da ke saman wayanka,
Domin idon har wayan tana neman "network" ko "service" to zata na dinga shan chajin wayanka batareda saninkaba Don haka ka kiyaye Kuma kabi wannan matakin sosai Don tanada muhimmanci.
2• Kubar sa wayarku a Aljihun wandon Jeans.
A ganinka hanya Mafi saukin da zakana yawo da wayanka shine sakawa a Aljihun wandon ka musamman wanduna na jeans , batareda saninkaba wasu Dotti da yan kananan abubuwa zasu shiga ramukan wayanka kamar na "charging pod" domin jeans yana rike Dotti da yan kananan kura da sauransu Don haka Koda sau nawa ka wanke baza su gama fitaba duka,
Wayannan dottin in sun shiga Ramin "charging pod" ka iya jawo mata matsala Wanda hakan zaisa battery Karan kanta tana rikici domin da "charging pod" da hakorin battery kusan a hade suke.
3• Kayi clear na apps da kashiga a gurin minimizing Kuma kana kulle DATA in baka Amfani da shi.
Kar kumanta clear apps a gurin minimizing ma'ana manhajojin da kayi amfani da su a ranan ka gogesu
Kuma kar ka manta da kulle DATA wayanka .
Wadannan abunda kake kallo ba komaiba sai su ja maka chaji ba kadanba .
4• Kadin ga kashe wayanka wani sa'in.
Wani sa'in yakamata kana kashe wayanka musamman dare inbaka sammanin na wani Kira Mai muhimmanci.
Kullum muna Amfani da wayarmu safe da Rana Wasu Kam suna yini suna amfani da wayansu,
Kamar yanda kowa na bukatan hutu misali in kadawo daga aiki zaka kwanta ka huta haka itama wayan ta bukatar hutu.
Kadan kashe ta akalla na minti sha biyar (15 ) Koda sau dayane a Rana.
Ammafa zaka aikata hakanne in wayanka tanada chaji sosai bawai inta saukaba,
Akalla sau uku a sati.
5• Kudaina Barin wayanku 100% .
Battery wayanku zata nakasa da wuri in har kuna Barin ta kullum a cike 100%
MISALI: Idan mutum yaci ya koshi sosai kasala zata kamashi ba zai iya aiki yanda Ake bukataba, haka itama waya take , Barin ta a 100% ba zata na ma Aiki mai kyau ba, ka dinga Barin wayan tana sauka kadan kadan kana bukatan ka da shi.
6• Kudaina Barin wayanku ya kwana yana chaji.
Wannan akidar ya kamata mu daina ta. Battery in ta cika Kuma ta na kan chaji Kai Kuma kana bacci to zata na aiki ko da ta cika hakan Kuma zai kawo ma battery nakasu,
domin Kai bazaka it's chankan lokaci da battery ta cikaba kana bacci.
Wannan ita ce hanya Mafi saurin nakasa batiri waya.
Don Allah ku bar Barin wayanku yana chaji ku Kuma kuna bacci.
7• Kubar Danna wayanku in ta a Chaji.
Mutane dayawa suna da wannan akidar na Danna waya lokacin da take yin chaji Kuma wannan babban kuskurene sosai ba kadanba, domin Amfani da waya lokacin da take chaji tana illata battery ba kadanba
Tana mata mugun illa , dalili kuwa kana chaji Kuma kana aiki
"Hausawa sunce: tafiya bazai hadu da Sosa duwawu ba"
Don haka ka daure ka hakura in yasamu chaji koda bai cikaba sai kayi abunda kakeso kayi da shi.
Amfani da waya lokacin da take chaji tana rage karfinta sosai a karshe zaka halaka battery na wayanka.
Anan muka kawo karshen wannan bayanai masu Amfani daga
Dan uwanku Abdulmajid Jibrilla Wanda akafi sanida MGK CEO na Shafin yanar gizo maisuna Wixardtech.com.ng
Zaku iya sambado Mana da tambayoyinku mukuma insha Allah zamu Amsamuku
Bissalam
Related Posts
Subscribe Our Newsletter



0 Comments to "Abubuwa 7 yakamata mutum ya bari in Yanason battery na shi ta jima [wixardtech.com.ng]"
Post a Comment